Episodios

  • Madubin Usman Kabara: Tallan Zango Na 1
    Jan 5 2026

    Daga yanzu Madubin Usman Kabara podcast zai dinga zuwa muku ne a tsarin shiri mai fitowa zango-zango, inda zamu saki zangon na 1 a mako mai zuwa ranar Juma’a 9 ga watan Janairun shekarar nan ta 2026.

    Kadan daga cikin bakin wannan zangon sun hada da:1. Prof. Abdalla Uba Adamu2. Umar M. Shareef3. Hon. Zainab Buba 4. Hon. Saudatu Sani5. Maryam Booth6. Zaaki AzzayKu yi following dina ta nan a kyauta don jin yadda mutane ke shan gwagwarmaya a rayuwa don mu koyi darasi ta hanyar ganin zurfin ruwa da na gaba.

    Más Menos
    3 m
  • Solomon Dalung | MUK Na 39
    Dec 22 2025

    Na sami zama tare da Lauya Dan Gwagwarmaya Barrister Solomon Dalung, tsohon Ministan Matasa Da Wasanni a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari. Inda na tattauna da shi don kallon rayuwarsa a cikin shirin Madubin Usman Kabara Podcast domin daukar darasi ga ‘yan baya.

    Más Menos
    32 m
  • Usman SojaBoy | MUK Na 38
    Dec 22 2025

    Na ziyarci Usman Umar (SojaBoy), domin yin hira da shi ido da ido a kokarina na jin dalilan salon wakokinsa da mafiya yawan mutane musamman 'yan Arewacin Najeriya, ba su yarda da salon nasa ba, suna ma kallon abin a matsayin rashin tarbiyya da rushe al'ada da addini.

    Más Menos
    40 m
  • Nazir Hausawa (Ziriums) | MUK Na 37
    Dec 22 2025

    Nazir Ahmed Hausawa (Ziriums), yana daya daga cikin ‘yan masana’antar finafinan Kannywood, Makadin Fiyano, Mawakin gambarar Hausa HipHop, Tsohon malamin koyar da kida, Tsohon ma’aikacin BBC World Service Trust da VOA Hausa, Masanin harkokin gidajen alfama na Amurka. A cikin hirarsa da Madubin Usman Kabara a Amurka, ya bayyana min darussan da ya koya a zamansa na shekaru a Amurka.

    Más Menos
    1 h
  • Nafisat Abdullahi | MUK Na 36
    Dec 20 2025

    Na sami yin hira da shahararriyar Jarumar Fina-finan Hausa Nafisat Abdullahi a birnin Washington DC da ke Amurka, don sanin asalinta da kuma yadda take tafiyar da rayuwarta.

    Más Menos
    1 h y 28 m
  • Barau I. Jibrin | MUK Na 35
    Dec 20 2025

    Na yi hira da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya, Mai Girma Sanata Barau I. Jibrin (Maliya) game da rayuwarsa da kuma gudunmawarsa a siyasance, musamman ga 'yan Arewacin Najeriya.

    Más Menos
    56 m
  • Kamaluddeen Kabir | MUK Na 34
    Dec 20 2025

    Kamaluddeen Kabir, dan asalin jigar Katsina ne mai digirin digirgir wanda yayi karatunsa a tsakanin Najeriya da Birtaniya sannan kuma Malami ne yanzu haka a jami'ar Umaru Musa 'YarAdua da ke jihar ta Katsina.

    Más Menos
    58 m
  • Aminu Waziri Tambuwal | MUK Na 33
    Dec 20 2025

    Mun sami tattaunawa Aminu Waziri Tambuwal gwamnan jihar Sokoto, kuma shugaban tawagar yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya a 2023 da ke tafe. Inda ya bamu labarin kuruciyarsa har zuwa girma da shiga fagen siyasa. Ba mu bar shi ba sai da ya fada mana dalilinsa na janye wa daga takarar shugabancin Najeriya don mara wa Atikun a karkashin jam'iyyar PDP.

    Más Menos
    29 m