Episodios

  • Yadda Takunkumin Amurka Zai Shafi Tattalin Arzikin ‘Yan Najeriya
    Dec 18 2025

    Send us a text

    Takunkumin da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wa wasu ‘yan Najeriya ya sake jawo hankali kan irin tasirin manufofin ƙasashen waje ga rayuwar mutane da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.


    Wannan takunkumi, wanda ya haɗa da hana shiga Amurka, da toshe kadarori ko hana mu’amala da wasu hukumomi da kamfanonin Amurka, ba wai hukunci ne ga mutum ɗaya kaɗai ba, kazalika yana da tasiri mai zurfi ga harkokin kasuwanci, zuba jari da martabar ƙasa a idon duniya.

    Ko ta yaya wannan takunkumi zai shafi tattalin arzikin daidaikun wadanda abun ya shafa, da ‘yan uwansu da ma Najeriya baki daya?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Más Menos
    16 m
  • Ce-ce Ku-ce Da Ya Dabaibaye Dauke Shalkwatar Bankin Masana’antu Zuwa Legas
    Dec 16 2025

    Send us a text

    Batun matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu zuwa jihar Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Wannan mataki ya tayar da mabanbantan ra’ayoyi daga bangarori daban-daban na al’umma, inda wasu ke kallonsa a matsayin shawara mai ma’ana da za ta karfafa harkokin masana’antu da jawo jarin cikin gida da na kasashen waje.


    Sai dai a daya bangaren kuma, akwai masu sukar wannan mataki, inda suma suka bayyana irin tasu damuwa kan batun.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan wadannan takaddama da kuma abun da kowanne gefe ke bayyanawa.

    Más Menos
    15 m
  • Matakan Da Jami’an Tsaro Ke Dauka Kan Tafiye-tafiyen Kirsimeti
    Dec 15 2025

    Send us a text

    A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama. Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukukuwa a garuruwa daban-daban, mutane da yawa yanzu suna cike da fargaba da damuwa. Babban dalilin hakan shi ne ƙalubalen tsaro da ke ƙara tsananta a sassa daban-daban.


    Rahotanni na hare-haren ’yan bindiga, da sace-sace a kan manyan hanyoyi, da garkuwa da mutane, da rikice-rikicen da ke faruwa ba zato ba tsammani, sun sanya mutane da yawa sake tunani kafin su ɗauki hanya da sunan zuwa bukukuwan karshen shekara. Wannan yanayi ya sa wasu ke zaɓar zama a garuruwan da suke, wasu kuma suna rage nisan tafiya ko sauya tsare-tsaren bukukuwansu gaba ɗaya.


    Ko yaya bukukuwan wannan shekarar za su kasance?

    Wadanne matakai hukumomi ke dauka don kare lafiyan matafiya?

    Wadannan da ma wasu tambayoyin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi kokarin amsawa.

    Más Menos
    15 m
  • Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
    Dec 11 2025

    Send us a text

    A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa.


    Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki a kan basira, da kirkire-kirkire, da koyon sana'o’i, domin shirya dalibai su zama masu amfani a harkokin tattalin arziki tun daga matakin makaranta.


    Shin ko wadanne alfanu ko akasin haka wannan canji zai haifar a fannin ilimi a kasar nan?
    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Más Menos
    15 m
  • Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba
    Dec 9 2025

    Send us a text

    A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suke taruwa a jikinsu har su zama guba ga mutum idan aka ci su.


    Wasu lokuta ma waɗannan gubobi ba daga abincin dabbar suke fitowa ba, sai dai daga sinadarai da ake amfani da su wajen kiwon su kamar magungunan kiwo, sinadaran rigakafi, ko ma gurɓatattun ruwa da suke sha.


    Shin ko ta wadanne irin hanyoyi alumma ke cin guba ta hanyar abincin da suke ci?

    Wadanne hanyoyi za a bi don magance afkuwar hakan?

    Wadannan da ma wasu tambayoyin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.

    Más Menos
    17 m
  • Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe
    Dec 8 2025

    Send us a text

    Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan.


    Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata don gudanar da dawainiyar ‘yansandan.


    Babban abun da jihohi ke bukata don samar da ‘yansanda shine kudaden gudanarwa don samar da wadannan abubuwa da na ambata.
    Ko nawa kowacce jiha ke bukata don samar da ‘yansanda?
    Ta wadannan hanyoyi za a bi don samar da wadannan kudade?
    Wadannan da ma wasu amsoshin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.

    Más Menos
    22 m
  • Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa
    Dec 4 2025

    Send us a text

    Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa.
    In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell?


    ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa.

    Ko yaya wannan dabara take aiki?


    Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari a kai.

    Más Menos
    25 m
  • Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta
    Dec 2 2025

    Send us a text

    Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.


    An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da wannan cuta. Abin damuwa shi ne cewa yawancin lokuta ana gano cutar ne a kurarren lokaci, wanda hakan ke sa magani ya yi wahala kuma ya rage yiwuwar ceto rayuwar wanda ya kamu da shi.


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Más Menos
    29 m