Episodios

  • Yadda Tattalin Arziki Da Ababen More Rayuwa Suke A Farkon Jamhuriya Ta Hudu Da Kuma Yanzu
    Jan 14 2026

    A shekarar 1999, lokacin da Najeriya ta sake komawa mulkin farar hula, tattalin arzikin ƙasa da kayayyakin more rayuwa na cikin wani yanayi na dogon mulkin soja.

    A wancan lokaci, masana da manazarta harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa dogaro da man fetur ya yi wa ƙasar katutu, masana’antu da dama sun tsaya cik, kuɗin ƙasa ya raunana, yayin da rashin aikin yi da talauci suka yi ƙamari. Haka kuma, a cewar manazarta, kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyi, da wutar lantarki, da asibitoci da makarantu sun lalace sakamakon shekaru na rashin kulawa.

    Yanzu kuma, bayan shafe fiye da shekaru ashirin da biyar da dawowar mulkin farar hula, ra’ayoyin manazarta sun kasu kashi biyu. Wasu na cewa an samu sauye-sauye a wasu fannoni na tattalin arziki da kuma gina kayayyakin more rayuwa, yayin da wasu ke jaddada cewa hauhawar farashi, da karyewar darajar naira, da wasu batutuwa da dama sun cigaba da yiwa kasar katutu.

    Ko yaya tattalin arziki da kayayyakin more rayuwa suke a lokacin da Najeriya ta dawo mulkin farar huka da kuma wannan lokaci?

    Wannan shine batun da shirin Daga Larba na wannan makon zai yi duba a kai.

    Más Menos
    26 m
  • Dalilan Da Suka Sa Matan Wannan Zamanin Ba Sa Son Talaka
    Dec 31 2025

    A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa.

    Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi.

    Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan matan wannan zamanin na kin auren talaka.

    Más Menos
    27 m
  • Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya
    Dec 17 2025

    Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai makamashi ba ne da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa; ginshiki ne da kusan dukkan harkokin tattalin arziki ke jingina da shi – daga sufuri, da samar da kayayyaki, har zuwa rabon su zuwa kasuwanni.


    Saboda haka, duk wani sauyi a farashin mai kan yi tasiri kai tsaye ko a kaikaice ga farashin kayan masarufi da ’yan Najeriya ke amfani da su a kullum, kamar abinci, da kayan gini, da magunguna da sauransu.

    Sai dai tambayar da ke yawan fitowa ita ce: shin rage farashin mai zai kai ga rage farashin wadannan kayayyaki?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Más Menos
    16 m
  • Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
    Dec 10 2025

    A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya.


    Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai.

    Más Menos
    14 m
  • Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
    Dec 3 2025

    Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar.


    Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci a yankuna daban-daban.

    Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban sabon ministan tsaron yayin da yake shirin kama aiki a ma’aikatar tsaro bayan majalisa ta tabbatar da shi?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    Más Menos
    28 m
  • Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
    Nov 26 2025

    A cikin 'yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.


    Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da 'yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi.
    Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu?


    Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a akai.

    Más Menos
    22 m
  • Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
    Nov 19 2025

    Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.


    Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba.


    Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.

    Más Menos
    28 m
  • Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma
    Nov 12 2025

    A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar.


    A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu.
    Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya?


    Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.

    Más Menos
    27 m
adbl_web_global_use_to_activate_DT_webcro_1694_expandible_banner_T1