Yadda Masu Larurar Ulcer Za Su Gudanar Da Azumin Ramadan Ba Tare Da Matsala Ba Podcast Por  arte de portada

Yadda Masu Larurar Ulcer Za Su Gudanar Da Azumin Ramadan Ba Tare Da Matsala Ba

Yadda Masu Larurar Ulcer Za Su Gudanar Da Azumin Ramadan Ba Tare Da Matsala Ba

Escúchala gratis

Ver detalles del espectáculo

Send a text

A duk lokacin da watan azumi ya zo, Musulmai da dama sukan karɓe shi da murna da shauƙi, suna shirya ibada da ƙara kusanci da Allah. Sai dai ga wasu, musamman masu fama da larurar gyambon ciki wato ulcer, watan azumi kan zo da wani yanayi na damuwa da fargaba. Yayin da wasu ke jin daɗin azumi, su kuma suna cikin ƙalubalen yadda za su iya jure yunwa da ƙishirwa ba tare da cutar ta tashi ko ta jawo musu matsananciyar wahala ba.


Ciwon ulcer na haddasa zafi a ciki, tashin zuciya, amai ko jin ƙuna musamman idan ciki babu komai na tsawon lokaci. Wannan ne ya sa azumi, wanda ke buƙatar jure yunwa daga asuba zuwa magariba, kan zama babban ƙalubale ga masu fama da wannan larura. Wasu kan kasa yin azumi gaba ɗaya, yayin da wasu ke fara shi amma su kasa kammalawa saboda tsananin ciwo.


Ko ta wadanne hanyoyi ne masu fama da wannan larurar zasu bi wajen yin azumi ba tare da sun sha wahala ba?

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kai.

Todavía no hay opiniones